Kungiyoyi farar hula sun mayar da martani kan yaki da kan cin hanci da rashawa a Nijer

A jamhuriyar Nijar, wasu kungiyoyin farar hula da na siyasa sun soma mayar da martani ga matakin da shugaban kasar, Alhaji Issoufou Mahamadou ya ce zai dauka, na kafa hukuma ta musamman wadda za ta yaki cin hanci da rashawa a kasar.

A farkon wannan makon ne shugaban ya bayyana haka a Malbaza, a jahar Tahoua, yayin kaddamar da ginin wani kamfanin siminti.

A cewar masu adawa da matakin, batun kafa hukumar yaki da cin hancin bai ma taso ba, tun da dai akwai hukumomin gwamnati masu binciken almundahna.

Yayin da bangare guda kuma ke cewa cigaba ne aka samu a kasar.