Obama ya gargadi shugabannin Sudan

Tashin wasu bama-bamai biyu a iyakar kudancin Sudan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashin wasu bama-bamai biyu a iyakar kudancin Sudan

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi kira ga shugabannin arewaci da kudancin Sudan su dakatar da fadan da suke yi a yankunan kan iyaka wadanda ake takaddama a kansu.

Shugaba Obama ya ce Amurka ta damu matuka da rikicin da ke ci gaba da ruruwa a Sudan, ciki har da fadan da ake gwabzawa a Kudancin Kordofan, wanda ya tilastawa dubban mutane tserewa daga gidajensu.

A wani nadadden sako da aka baiwa gidan Rediyon Muryar Amurka, Shugaba Obama ya ce:

“Ba matakan soji ba ne mafita—wajibi ne gwamnatin Sudan ta kaucewa kazancewar wannan rikici ta hanyar dakatar matakan soji nan take; ta dakatar da kai hari ta jiragen sama, da tilastawa mutane barin gidajensu da kuma muzgunawa”.

Shugaba Obama ya kuma gargadi bangarorin biyu da cewa duk wanda ya gaza bayar da wajibinsa kamar yadda yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma ta tanada, to zai fuskanci matsin lamba, kuma za a mayar da shi saniyar-ware.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da shugabannin na Sudan za su nuna bajinta da hangen nesan da ake bukatar gani ga shugabanni na kwarai, su zabi zaman lafiya.

Karin bayani