Rayuwar mata na cikin hadari a Afghanistan

Matan Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Matan Afghanistan a wurin wani taro bara

Wani sabon bincike, wanda masana al'amuran da suka shafi jinsi suka gudanar, ya bayyana Afghanistan a matsayin kasar da ta fi hadari ga rayuwar mata a duniya.

Binciken, wanda Cibiyar Thomson Reuters ta kasar Burtaniya ta gudanar, ya nuna cewa yawaitar tashe-tashen hankula, da karancin ingantattun hanyoyin kiwon lafiya, da kuma fatara ne suka taru suka haddasa yanayi mafi hadari ga mata a kasar ta Afghanistan.

A lokacin binciken dai, an bukaci masana daga nahiyoyi biyar na duniya su dari biyu da goma sha uku su jera kasashen da mata suka fi fuskantar hadari.

Daga cikin hadurran da aka duba akwai wadanda dalilai na addini da al'ada suka haifar; da kuma samun damar amfana da abubuwan more rayuwa, da matsalar safarar mata.

Binciken ya gano cewa mata na fadawa cikin hadari a Afghanistan din duk kuwa da sa hannun kasashen Yamma a al’amuran kasar.

Kasashen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Pakistan ne suka rufawa Afghanistan din baya a matsayi na biyu da na uku.

Ita kuwa Indiya, wacce ita ce kasar da ta fi yawan al'umma a tsakanin kasashen duniya masu bin tafarkin dimokuradiyya, ita ce ta hau matsayi na hudu a jerin kasashen da ke da hadari ga rayuwar mata; ta kuma samu wannan matsayi ne musamman saboda yawan kashe 'ya'ya mata da ake yi da kuma yawan karuwanci.

Sai kuma matsayi na biyar inda aka sanya Somaliya, kasar ta kwashe kusan shekaru ashirin ba ta da tsayayyiyar gwamnati.