Amurka ta ce za ta farauto al-Zawahiri

Admiral Mike Mullen Hakkin mallakar hoto d
Image caption Admiral Mike Mullen

Shugaban Majalisar Hadin Gwiwa ta Hafsoshin Sojin Amurka ya ce kasar za ta farauto sabon jagoran kungiyar Al-Ka'ida, Ayman al-Zawahiri, ta kuma kashe shi kamar yadda ta kashe Osama bin Laden.

Admiral Mike Mullen ya kuma ce bai yi mamakin zabar Ayman al-Zawahiri ya gaji Osama bin Laden ba.

“A gani na ba abin mamaki ba ne da Zawahiri ya gaje matsayin bin Laden.

“Har yanzu shi da kungiyarsa suna barazana ga Amurka don haka kamar yadda muka yi nasarar farauta da kuma kisan bin Laden haka ma za mu yi a kan Zawahiri”, in ji Admiral Mullen.

Sakataren tsaro na Amurkan dai, Robert Gates, ya ce Ayman al-Zawahiri ba shi da kwarjini da iya jagoranci irin na bin Laden, amma duk da haka nadinsa a matsayin shugaban kungiyar Al-Ka’ida tunatarwa ce cewa har yanzu kungiyar na da tasiri.

Mista Gates ya kara da cewa ko da ya ke Zawahiri zai fuskanci kalubakle da dama, Amurka za ta ci gaba da farautar 'ya'yan kungiyar ta Al-Ka’ida.

Shi dai Ayman al-Zawahiri tsohon na hannun daman Osama bin Laden ne kuma shi ne mutum na biyu mafi girma a kungiyar Al-Kaida.

Kungiyar ta Al-Ka’ida dai ta sha alwashin ci gaba da yakin da ta ke yi da Amurka da Isra'ila da kuma sauran kawayen Amurkar.