Kotu za ta yanke hukunci kan tattaunawa a Facebook

Kotu za ta yanke hukunci kan tattaunawa a Facebook Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karo na farko da ake yin irin wannan shari'a

Wani mai taimakawa alkali da ya tattauna da wanda ake zargi a shafin Facebook, ya aimnce cewa ya sabawa umarnin kotu a wata shari'a irinta ta farko a Burtaniya da ta shafi intanet.

Babbar kotun birnin London ta samu labarin cewa Joanne Fraill, 'yar shekaru 40, ta tattauna da Jamie Sewart, dan shekaru 34, wanda aka wanke daga laifi a shari'ar miyagun kwayoyi a garin Manchester.

Sai dai har yanzu mai taimakawa alakli na duba yiwuwar tuhumar daya mutumin da ake zargi kuma ganawar ta sa alkali ya kori mai taimaka masan, kuma shari'ar ta watse.

An samu Sewart da aikata abin da ka iya zamowa sabawa umarnin kotu.

Ta amince cewa tattaunawar ta faru, amma ta musanta cewa ta aikata wani laifi.

Mutanen biyu na fuskantar zaman gidan yari na shekaru biyu idan aka yanke musu hukunci.

Shari'ar wacce babban mai gabatar da kara Dominic Grieve QC ya gabatar, mai shari'a Lord Judge, da wasu alkalai biyu ne ke saurarar ta. Fraill ta ce ta tattauna da Sewart ta shafin intanet na Facebook, kuma sun tattauna ne a lokacin da masu taimakawa alkali ke ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.

Ta kuma bayyana yadda tattaunawar masu taimakawa alkalin ta ke gudana a hirar da suka yi a intanet din - wanda hakan ya kaucewa dokar sabawa kotu ta 1981 - da gudanar da bincike a intanet kan wanda take taimakawa alkali a shari'arsa.

Wannan kuwa ya faru duk da yadda alkalin ke tunasar da masu taimaka masa cewa dole ne su yanke hukunci ta hanyar amfani da bayanan da aka gabatar a kotu.

A wani jawabi da ya yi bara, babban alkali ya gargadi masu taimakawa alkalai cewa za su iya samun kansu a gidan yari idan suka nemi bayanan wadanda ake kara a intanet.

A lokacin jawabin, ya ce ya san shari'ar da ake yi kan fyade wacce aka dakatar saboda binciken da masu taimakawa alkali suka gudanar a intanet.

"Har yanzu ana tantama kan mai taimakawa alkali ya yi amfani da intanet wajen neman bayanai kan wata shari'a sabawa doka ne, kuma laifi ne," a cewarsa.