Shugaban Senegal ya ziyarci 'yan tawayen Libya

Shugaba Abdullai Wade
Image caption Kan Afrika ya soma rabuwa a kan Libya

Kungiyar yan adawar Libya ta karbi alkawarin samun dola fiye da biliyan daya a wajen wani taro na kungiyar kasashe masu ruwa da tsaki kan Libya a Abu Dhabi.

Kasar Italiya ta ce za ta bayar da gudumawar Dola miliyan 6 sannan Kuwaiti ta yi alkawarin karin miliyan dari da 80.

Faransa ta ce za ta bayar da dola miliyan 400 a cikin mako daya, daga cikin kudaden Libyar da ta kwace.

Majalisar gudanarwar wucin gadi ta yan adawa -- wadda ke jagorantar boren da ake yiwa Kanar Gaddafi -- ta ce tana bukatar biliyan uku domin biyan albashi da sayen kayan abinci domin watanni masu zuwa.

Ministan harkokin wajen hadaddiyar daular larabawa, Sheikh Abdullah Bin Zayed Al-Nahya ya ce kungiyar kasashen masu ruwa da tsaki a kan Libya na duba hanyoyin sakin karin kudi ga ‘yan adawar,

Ya ce, yana da muhimmanci matuka a fahimci cewar wannan wata hanya ce da ke duba gudumawar kasashe.