Liverpool ta kammala sayen Jordan Henderson

Jordan Henderson
Image caption Jordan Henderson na murnar wata kwallo da ya zira a Sunderland

Liverpool ta kammala sayen dan wasan Sunderland Jordan Henderson bayanda kungiyoyin biyu suka cimma matsaya.

Dan wasan na Ingila mai shekaru 20 ya kammala gwajin lafiyarshi sannan ya amince da tayin da Liverpool suka yi masa a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana kudin da aka sayi dan wasan da cewa sun kai fan miliyan 20.

Henderson, wanda shi ne dan wasa na farko da kulob din ya saya a kakar bana, ya sanya hannu kan abinda Liverpool suka bayyana da cewa 'doguwar yarjejeniya'.

"Na yi matukar farin ciki da zuwa na nan, kuma a shirye nake na taka leda," kamar yadda Henderson ya shaidawa shafin intanet na Liverpool.