Majalisar dokokin Nijar ta samu koma-baya a kotu

Tutar Nijar
Image caption Tilas majalisar ta sake nazari

A jamhuriyar Nijar kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da wani shiri na yan majalisar dokoki masu rinjaye na kirkiro wasu sabbin mukamai biyu a kwamitin gudanarwa na majalisar da suka hada da mukamin mai ajiya da na sakataren majalisar.

A cewar kotun, dokokin tsarin majalisar ba su bayar da hurumin yin hakan ba.

Da ma 'yan adawa sun yi Allah wadai da shirin tun farko suna masu cewa ya saba ma doka.

‘Yan majalisar masu rinjayen dai sun ce za su aiwatar da umurnin kotun.

Ko a kwanakin baya ma an taba samun irin wannan takon saka tsakanin yan majalisar masu rinjye da kotun tsarin mulkin.