An sabunta: 9 ga Yuni, 2011 - An wallafa a 10:05 GMT

Ra'ayi Riga: Dokar yaki da ta'addanci a Najeriya

Wani hari da aka kai a Maiduguri

Ana samun hare-haren ta'addanci da dama a Najeriya

A kwanannan ne shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya sanya hannu kan dokar yaki da ta'addanci a kasar wacce ake saran za ta taimaka wajen inganta tsaro a kasar.

Ana kuma saran za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin jama'a da tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu.

Sai dai wasu 'yan kasar na nunu shakku kan irin tasirin da dokar za ta iya yi wajen hana ayyukan ta'addanci.

To kufa menene naku ra'ayin kan wannan dokar. Kadan kenan daga cikin irin abubuwan da za mu tattauna a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

To sai ku aiko mana da ra'ayoyinku ta adreshinmu na email, wato hausa@bbc.co.uk, ko ta lamba 44 77 86 20 20 09, ko kuma ta dandalin mu na muhawara, wato BBCHausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na internet, wato bbchausa.com.

Ko kuma ta hanyar cike wannan gurbin:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.