'Yan Taliban sun kashe sojoji takwas

taliban Hakkin mallakar hoto BBC NEWS
Image caption Dan yakin sa kai na Taliban

Mayakan Taliban fiye da dari ne dauke muggan makamai suka kai wani hari kan shingen binciken yan sanda a kudancin Waziristan na kasar Pakistan inda suka halaka sojoji a kalla takwas.

A kalla mayakan guda 12 ne suka rasu.

An kai harin ne a yankin Makeen, wanda ya kasance daya daga cikin wurarenda ake taho mu gama tsakanin dakarun Pakistan da mayakan Taliban.

Harin ya faru ne a tsakar dare. 'Yan Taliban da dama dauke da bindigogi da rokoki suka diramma shiggen binciken sojoji.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sojojin Pakistan nan take suka maida martani inda aka yi musayar wuta na tsawon fiye da sa'o'i uku.

A shekara ta 2009 dai sojojin Pakistan sun yi luguden wuta a kudancin Waziristan, amma 'yan yakin sakai na Taliban basu daina kai hare hare ba.

Wannan harin na baya bayan nan na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka ke kara matsa kaimi wajen diranma yankunan kabilun dake kusada kan iyakar Pakistan da Afghanistan.