Gandiroba ba sa kashe 'yan boko haram

Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya reshen jihar Borno ta musanta zargin da ake yi mata na aikata kisan mummuke kan wasu daga cikin 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da take tsare da su.

Tun a makonnin baya ne dai jama'a suka fara zargin cewa jami'an gidan yarin na Maiduguri na aikata hakan ta hanyar sa musu dafi a abinci.

Tun dai bayan fara wannan zargi ne ma'aikatan gidan yarin na Maiduguri suka fara fuskantar barazanar kai hare hare da kashe-kashen da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka yi ikirarin su ke aikatawa.

Hukumar Gidan yarin dai ta ce ta yi asarar rayukan ma'aikatanta kimanin shida a hare-haren na baya-bayan nan, yayin da wasu da dama ke ci gaba da fuskantar barazana a gidajen su.