Watakila sojojin Amurka su cigaba da zama a Iraki

sojoji Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sansanin sojojin Amurka a Iraki

Akwai yiwuwar kasar Iraki ta bukaci Amurka ta cigaba da zama a kasar fiye da karshen wannan shekarar, lokacin da sojojin Amurka aka tsara zasu bar kasar.

Wannan maganar ta fito daga wajen Leon Panetta wanda aka zaba don zamowa sakataren tsaron Amurka.

Ya kuma bayyana haka ne a wajen sauraron ba'asi na majalisar datijjan Amurka akan sabon mukamin.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana kuru kuru cewar tanason ta ajiye wasu daga cikin sojojin Amurka 46,000 a Iraki su zauna fiye da karshen wannan shekarar don taimakawa dakarun Iraki sun magance matsalar tsaron da kasar ke fama dashi.

A wani mataki tamkar matsin lamba ga Irakin, jami'an Amurka sun nanata cewar a yanzu ya rage ga gwamnatin Iraki ta nemi bukatar hakan.

Leon Panetta wanda a nan gaba za a tabbar a matsayin sakataren tsaron Amurka, ya ce yanada tabbacin cewar Iraki zata nema sojojin Amurka sukara wa'adin zamansu a can.

Koda yake dai bai bayyana adadin sojojin da za'a bukaci su cigaba da zaman ba ko kuma abinda zasu dinga yi, amma dai ga alama Amurka ko kokarin kwadaitar da Iraki ne.

Sai dai babu tabbas ko shugaba Obama zai amince sojojin Amurka su cigaba da zama a Iraki, saboda matakin tamkar yayi amai ya lashe ne ganin irin kwarin gwiwar daya bayar cewa daukacin sojojin Amurka zasu fice daga Iraki a bana.