Gwamnatin Jigawa ta gaza wajen samarda ruwa

jigawa
Image caption Gwamnan Jigawa Sule Lamido

Kokarin samarda wadataccen ruwan sha mai tsafta ga jama'a na daga cikin kudurin majalisar dinkin duniya na muradun karni da wanda kuma mahukunta a Najeriya ke fatan tabbatarwa nan da shekara ta 2015.

Yayin da mahukunta suka maida hankali wajen cimma wannan buri, da alamu akwai sauran aiki a gaba, musamman idan akayi la'akari da yanayin da mazauna yankunan karkara ke ciki, musamman a kasashen masu tasowa.

Al'ummar kauyen Fadi Bara a jihar Jigawa sun ce gwamnati na gaza cika alkawarin data dauka wajen samarda tsabtattacen ruwansha a kauyen duk da alkawarin data dauka lokacin zabe.

A cewar mazauna kauyen ruwan da akan samu daga rijiyar kwakware bai yiwuwa ayi girki da shi don yana canza dandanon abinci.