Amurka ta nuna damuwa kan China

Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption China na barazana ga huldar da ke tsakanin Amurka da Afirka

Sakatariyar hulda da kasashen wajen Amurka, Hillary Clinton ta bayyana matukar damuwa ga yadda huldar kasuwanci ke habaka tsakanin China da kasashen Afirka.

A jawabin da ta yi a Zambia, a matakin farko na ziyararta ta kwanaki biyar a kasashen, Hillary Clinton ta ce, yadda China ke bayar da tallafi da zuba jari a Afirka ya gaza ka'aidojin kasashen duniya.

China dai na amfani ne da albarkatun Afirka wajen bunkasa tattalin arzikinta, kana tana samar da abubuwan more rayuwa ga kasashen na Afirka.

Sai dai Amurka na ganin hakan na barazana ga huldar da ke tsakaninta da kasashen Afirkan.