Za a biya diyya ga 'yan kasar Columbia

Shugaban Columbia, Mr Santos, da sakataren majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Columbia za su karbi diyya

Shugaban Columbia, Juan Manuel Santos ya sanya hannu akan dokar da za ta sanya a biya diyya ga mutane kimanin miliyan hudu da rikicin kasar na kusan shekaru arba'in ya shafa.

Dokar, wacce shugaba Santos ya ce tana cike da tarihi, za ta samar da diyya ga dangogin wadanda rikicin kasar ya shafa, da kuma maida filaye da aka kwace ga ainihin masu su.

Shugaban ya ce za a baiwa mutanen fiye da dala biliyan ashirin.

Sai dai masu lura da al'amura na cewa, aiwatar da dokar zai zama wani babban kalubale da zai kwashe kusan shekaru goma, kasancewa gwamnati ta ce bata da kudi.

Babbab sakataren majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon wanda ya halarci wajen sanya hannu kan dokar, ya ce hakan wata hanya ce ta magance rikicin da kasar ta yi fama da shi.