Tallafi kan ambaliyar ruwa a Kebbi

Taswirar Najeriya
Image caption Ana bayar da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa

Mahukunta a jihar Kebbin Najeriya na cigaba da raba kudin tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa.

Dubban mutane ne dai suka yi asarar muhallinsu, da kuma kayan abinci a jihar sakamakon bala'in ambaliyar ruwan da ta aukawa jihar a bara.

Wannan tallafin dai ya fito ne daga gwamnatin tararayya, da na jahohin kasar, da kuma wasu hukumomi daga ciki da wajen kasar.

Sai dai wadanda ke karbar tallafin na nuna damuwa akan yawan kudin da hukumomin ke basu, yayin da wasunsu ma suka ce ba a basu ba.

Dama dai wadanda bala'in ya shafa sun jima suna kokawa kan tsaikon da aka yi kafin soma rarraba tallafin.