'Yan tawaye na kai farmakin martani a Zawiya na Libya

'Yan tawaye a Libya na ci gaba da kai farmaki a kokarin sake karbe iko da wani muhimmin gari daga dakarun gwamnati a yammacin kasar.

Wani mai magana da yawun 'yan tawayen ya ce an shiga kwana na biyu ana mummunan artabu tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a garin Zawiyah, mai muhimman wuraren tara mai, wanda kuma bai wuce tafiyar sa'a guda ba cikin mota, zuwa birnin Turabulus.

wakilin BBC ya ce, rahotanni na cewa, 'yan tawayen sun sake kame wani bangare na Zawiyya, suna kuma yunkurin kai wa ga sauran sassansa.

Akwai kuma wani artabun, a kudu da birnin na Turabulus, a garin Yefran da kewayensa.

Rikicin na Libya dai ya soma haifar da matsaloli a Jamhuriyar Nijar.

Hukumomin kasar Niger din dai sun tabbatar a yau cewar, an soma samun bazuwar makamai, harma da wasu hare hare da suke zargin wasu da suka fito daga kasar ta libya ne ke kai su.

Alkaluman hukumomin Niger din na wannan wata na Yuni sun ce mutane akalla dubu dari da goma sha biyar suka shiga kasar ta kasa, ta garuruwan Dirkou da Agadez a arewacin kasar daga Libyar.