Yau ake tunawa da zaben 12 ga watan Yunin 1993 a Najeriya

Ana gudanar da wasu ke tarukan tunawa da zaben ranar sha biyu ga watan Yunin 1993 a Najeriya.

zaben da mutane da yawa suka yi amannar cewa marigayi Cif Mashood Abiola ne ya lashe shi, amma hukumomin soja, karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida suka soke shi.

A ciki da wajen Najeriya dai wasu sun yaba ma sahihincin zaben shugaban kasar na sha biyu ga watan Yunin a matsayin wanda ya kyautata hadin kan kasar.

A lokacin wannan buki dai wasu kungiyoyin fararen hula masu rajin kare mulkin demokradiya sun zayyana wasu abubuwa da suke ganin ya kamata a yi domin tunawa da marigayi Cif Abiola.

Bukin na yau ya fi tasiri ne asashen kudu maso yammacin Najeriya.