Bam ya halaka mutane talatin a Pakistan

Wasu mata suna kuka sakamakon harin da aka kai a Pakistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bam ya halaka mutane a Pakistan

Tashin bama-bamai biyu a arewacin Pakistan ya haddasa mutuwar mutane fiye da talatin, yayin da wasu mutanen fiye da dari suka jikkata.

Bama-baman biyu dai, sun tashi ne da tazarar mintuna kalilan a wata kasuwar birnin Pashewar da ke cike makil da jama'a.

Wannan hari dai shi ne na baya-bayan nan, a ci gaban farmakin da masu tsaurin ra'ayi da ke dauke da makamai ke kaiwa jami'an tsaro da ma fararen hula.

'Yan sanda sun tabbatar da cewa, dan kunar-bakin-wake ne ya tayar da daya daga cikin bama-baman.