Yau ake gudanar da zabe a Turkiya

Recep Tayyip Erdogan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana gudanar da zabe a Turkiya

Jama'a a kasar Turkiya sun soma kada kuri'a a zaben kasa baki daya a yau Lahadi, wanda zai iya baiwa Firayi Minista, Tayyip Erdogan damar samun wa'adin mulki na uku.

Jam'iyyar AKP ta Mista Erdogan, mai sassaucin ra'ayin Islama za ta fuskanci babban kalubale ne daga jam'iyyar CHP wadda ba ta danganta kanta da addini.

Shi dai Mista Erdogan, ya yi alkawarin aiwatar da sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar da aka amince dashi a kuri'ar raba-gardamar da aka yi a watan Satumbar da ya gabata.

Gabanin zaben na yau dai, jam'iyyun siyasar kasar sun yi ta sukan juna.