An kaddamar da shirin riga-kafin cutuka.

Hamshakin attajiri, Bill Gates
Image caption Hamshakin attajiri, Bill Gates

Masu bada agaji na kasashe sun sha alwashin samar da dala biliyan hudu da miliyan dari ukku, domin gudanar da shirye-shiryen rigakafi a kasashe masu tasowa.

An yi wannan albishir ne a lokacin taron da aka gudanar yau, a birnin London, kuma masu bada gudummawar sun hada da gwamnatoci, da kuma masu zaman kansu - ciki har da hamshakin attajirin nan na Amurka, Bill Gates.

Kamfen din zai maida hankali ne wajen yaki da ciwon kirji - ko pneumonia - da kuma gudawa, wadanda suna daga cikin cututtukan da suka fi hallaka kananan yara.