EFCC ta sake kai Bankole kotu bayan an bada belinsa

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, EFCC, ta sake gurfanar da tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole, a wata babbar kotun ta dabam da ke Abuja, bayan kotun da ke masa shari'a akan wasu zarge zarge goma sha shidda, ta bada belinsa a yau.

EFCCn ta gurfanar da Dimeji Bankolen ne, tare da tsohon mataimakinsa, Usman Bayero Nafada.

Tana tuhumarsu da aikata wasu sabbin laifuka goma sha bakwai da suka shafi karbar rancen tsabar kudi Naira miliyan dubu talatin da takwas daga banki, don gudanar da wasu hidimomin majalisar, tare da kara wa `yan majalisar kudaden alawus ba bisa ka`ida ba.

Mutanen biyu dai sun musanta zarge zargen.