Hukumar SSS ta ce ba a coci aka kai hari ba

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Jihar Borno da ke arewacin Najeriya, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, wato SSS, ta fitar da wata sanarwa da yammacin ranar Juma’a a kan harin bom din da aka kai a garin Damboa, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar yara hudu tare da jikkata wadansu.

Sanarwar ta hukumar SSS ta ce tabbas bom ya tashi a Damboa ranar Talata, 16 ga watan Yuni, amma a wani gida sabanin labarin da wadansu kafofin yada labarai ke bayarwa—cewa an kai harin ne a kan majami’ar EYN.

Ta kuma ce gaskiya ne mutane hudu sun rasu—wadansu kananan yara wadanda ke wasa a tsakar gidan da bom din ya fashe.

Amma, a cewar hukumar ta SSS, ko kadan bom din bai shafi majami’ar ba.

Hukumar ta ce tana ganin alamun bayanan da kafofin yada labarai ke bazawa suna neman haifar da rudani a Jihar wadda ke fama da matsalar tsaro.

Wannan ne dai karo na farko da hukumar ta SSS ta fitar da sanarwa wadda ta danganci mawuyacin yanayin tsaron da ya addabi jihar ta Borno.