Tsohon shugaban Zambia, Chiluba, ya rasu

Frederick Chiluba da matarsa
Image caption Marigayi Frederick Chiluba da matarsa lokacin da kotu ta wanke shi

Tsohon shugaban kasar Zambia, Frederick Chiluba, ya rasu yana da shekaru sittin da takwas.

Mista Chiluba ne dai shugaban kasar ta Zambia na farko da aka zaba a bisa tsarin dimokaradiyya, ya kuma jagoranci kasar har tsawon shekaru goma.

Marigayi Frederick Chiluba ya zama shugaban kasar Zambia ne, a shekarar 1991, a daidai lokacin da wani sabon zamani na tsarin dimokaradiyya mai jam'iyyu da yawa ya fara bayyana a kasashen Afirka.

A matsayinsa na tsohon jagoran ’yan kwadago a kasar, Mista Chiluba ya hau gadon mulki ne da alkawarin kawo sauyi.

A farkon hawansa kuma, Mista Chiluba, wanda ake yiwa kallon gwarzon dimokaradiyya a nahiyar Afirka ta wancan lokacin, ya fadada 'yancin da al'ummar ke da shi.

Sai dai kuma daga baya ya yi ta daukar salon mulkin wanda ya gada, wato Kenneth Kaunda—ya yi ta kokarin danne 'yan adawa.

Ya kuma kyale cin hanci da rashawa sun samu gindin zama a kasar; sannan ya sha suka saboda irin rayuwar da ya ke yi ta kasaita.

Shugaba Chiluba ya kuma gamu da zazzafar adawa daga al'ummar kasar lokacin da ya yi yunkurin sake darewa gadon mulki a karo na uku.

Bayan ya sauka daga mulki a shekarar 2001, wanda ya gaje shi, Levy Mwanawasa, ya tube masa rigar kariya daga tuhuma, sannan ya kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa.

Bayan an kwashe shekaru shida ana tafka shari'a da Chiluba a bisa zarginsa da laifin yin ruf-da-ciki a kan dukiyar al'umma, kotu ta wanke shi daga duk wani laifi.

Mista Chiluba dai ya ce wannan zargi ba komai ba ne illa bi-ta-da-kulli.

Sai dai a wata shari'ar ta daban, a shekarar 2007 Babbar Kotun birnin Landan ta same shi da laifin yin almubazzaranci da miliyoyin daloli na kasar ta Zambia.