Sojin Korea ta Kudu sun harbi jirgin fasinja

Lee Myung-bak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Korea ta Kudu, Lee Myung-bak

Sojojin Korea ta Kudu sun ce sun budewa wani jirgin saman fasinja wuta, bayan da suka yi kuskuren daukar sa a matsayin jirgin saman sojin Korea ta Arewa.

Jami'an kasar dai sun ce babu wata asara da ta biyo bayan bude wutar da sojoji biyu suka yi a kan jirgin na kamfanin Asiana Airlines.

Kamfanin dillancin labaran Korea ta Kudu ya ce sojojin sun harba harsasai casa’in da tara, sai dai jirgin ya haura iya nisan da harsasan za su iya kaiwa, don haka ne har ya sauka ba tare da matsala ba.

Jirgin, wanda ya taso daga China, yana dauke da fasinjoji fiye da dari.