'Yan tawayen Libya na fasa-kwaurin makamai

Ana bincike kan yiwuwar shigar da makamai Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawaye na shigar da makamai cikin Libya

'Yan tawayen Libya suna fasa kwaurin makamai ta iyakar kasar da Tunisia domin su yaki dakarun Kanar Gaddafi a yammacin kasar.

Wani mai yin fasa-kwaurin makaman da baya so a ambaci sunansa ya fadawa BBC cewa, 'yan tawayen na shigar da bindigogi kirar AK-47, da kuma makaman harba gurneti zuwa Libya ta kan iyakarta da Tunisia.

Wakiliyar BBC ta ce, 'yan kasar ta Libya da ke zaune a kasashen waje ne ke samar da kudaden da ake amfani da su wajen sayen kananan makamai da ake yin sumogarsu zuwa cikin Libya.

Wakilin BBC a kan iyakar Libya da Tunisia ya ce, kungiyoyi masu zaman kansu da dama sun nuna damuwa ga yadda ake fasa kwaurin makaman zuwa Libya.