Sarkin Morocco zai rage ikon da ya ke da shi

Sarki Mohammed
Image caption Sarki Mohammed na Morocco

Sarki Mohammed na Morocco ya bayar da sanarwar wadansu sauye-sauye wadanda za su rage dimbin ikon da ya ke da shi, sannan su karawa firayim minista da majalisar dokoki karfi.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba kasar Morocco za ta zamo mai bin tafarkin dimokaradiyya a karkashin jagorancin kundin tsarin mulkin kasa da majalisar dokoki.

Gidan Sarautar Morocco ne dai gidan sarautar da ya fi ko wanne dadewa a kasashen Larabawa.

Sai dai kamar sauran kasashen na Larabawa, guguwar sauyin da ke kadawa a yankin ta girgiza kasar ita ma.

A jawabin da ya yi ta gidan talabijin na kasar, Sarki Mohammed na Shida ya yi alkawarin shirya wata kuri'ar raba-gardama don neman amincewar al'ummar kasar a kan wadannan sauye-sauyen.

Musamman, sabon kundin tsarin mulkin zai yi tanadin cewa daga yanzu jam'iyyar da ta yi nasara a zabe ce za ta nada firayim ministan ba Sarkin ba; sai dai ya ce shi ne zai ci gaba da kasancewa hafsan koli na askarawan kasar.

Akasarin mutanen kasar dai sun nuna gamsuwa da wannan sanarwa, amma wadansu na ganin cewa kundin tsarin mulkin da ake shiryawa ba na dimokuradiyya ba ne.

Ranar daya ga watan Yuli ne dai ake sa ran gudanar da kuri'ar raba-gardamar a kan sauye-sauyen.