'Yan gudun hijira daga Syria na kara kwarara Turkiyya

Ana cigaba da samun karuwar 'yan gudun hijira wadanda suke gujewa rikicin da ake yi Syria, inda rahotanni suka ce yanzu haka kimanin mutane dubu bakwai sun tsallaka zuwa kasar Turkiyya, sannan karin wasu na tahowa.

Jami'an kasar Turkiyya suna karbar 'yan gudun hijirar ne a wasu sansanoni guda hudu.

Jama'ar da suke tsallakawa zuwa kan iya sun ce sojojin kasar Syria suna tsare daruruwan mutane a kauyukan dake kusa da garin Jisr al Shughour, wanda sojoji suka kwace bayan wani bore kimanin mako guda kenan.