'Tattalin arzikin Gaza ya tabarbare'

Shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yanayin tattalin arziki a yankin Gaza

Majalisar dinkin duniya ta fitar da rahoto kan yanayin tattalin arzikin yankin Gaza, inda ta ce tattalin arzikin yankin ya yi matukar tabarbarewa.

Rahoton dai, ya yi nazari kan yanayin tattalin arzikin yankin ne, tun bayan da Israela ta tsaurara killacewar da ta yi masa a shekarar 2007.

Rahoton ya ce akalla, a cikin dukkan mutane biyu da ke yankin, mutun guda bashi da aikin yi.

Kazalika rahoton, ya ce kudaden shiga da mutane ke samu sun ragu da fiye da kaso uku cikin dari, a cikin shekaru biyar din da suka gabata.

Ita dai Israela, ta tsaurara killacewar da take yiwa yankin Gaza ne tun daga shekara 2007, bayan da kungiyar Islama ta Hamas ta fara mulki a yankin.

'Hamas ta taka rawar-gani'

Sai dai duk da haka, rahoton na majalisar dinkin duniya , ya ce gwamnatin Hamas ta aiwatar da sauye-sauyen da suka kawo bunkasar tattalin arziki a wadansu sassan yankin.

Hakan ya faru ne, bayan da ta baiwa dubban mutane aikin yi.