Za a fara shari'a kan tsohon shugaban Tunisia

Ben Ali Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a fara shari'a kan Ben Ali

A ranar Litinin mai zuwa ne za'a fara yiwa tsohon shugaban Tunisia, Zine Al Abidin Ben Ali shari'a duk da cewa ba ya kasar.

Shi dai tsohon shugaba Ben Ali ya tsere zuwa kasar Saudiyya ne, bayan jama'ar kasar sun tilasta masa sauka daga kan mulki wanda ya shafe shekaru ashirin yana yi.

Akwai wadansu jerin bincike da ake gudanarwa akansa- da kuma iyalansa- inda ake zarginsu da aikata kisa, da amfani da mukami ba bisa ka'ida ba, da zamba cikin-aminci, da kuma sace kayayyakin tarihin kasar,wadanda suka kai kasashen waje.

Shi dai Ben Ali bai fito bainar jama'a ba, tun bayan da ya fice daga kasar, kuma iyalansa sun ce yana fama da matsalar shanyewar bangaren jiki.

Sai dai a cikin wata sanarwa da tsohon shugaban ya fitar, ta hannun lauyansa da ke Faransa, ya bayyana zarge-zargen da ake yi masa da cewa, wani shifcin gizo ne kawai.