Vietnam na gudanar da atisayen sojoji

Wasu 'yan Vietnam suna zanga-zanga kan China Hakkin mallakar hoto Reuters

Kasar Vietnam tana gudanar da atisayen horo da ya hada da wasan wuta a tekun kudancin China.

Hakan na faruwa ne, a yayin da zaman dar-dar ke karuwa tsakaninta da China akan wani bangare na teku da ake zaton yana da rijiyoyin mai.

Wani jami'in sojan ruwan Vietnam ya ce, atisayen irin wanda aka saba yi ne, kuma ana yinsa ne a wurin da ya ke da nisan kilomita arba'in daga yankin Qag Nam na tsakiyar kasar ta Vietnam da ake rikici akansa.

Kafar yada labarai ta gwamnatin China dai ta ce, atisayen sojan Vietnam na nuni da yunkurin bijirewar da kasar ke son yiwa China.