'Yan bindiga sun yi artabu da jami'an tsaro a Arlit

Hukumomin Nijar sun ce, akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, a taho-mu-gamar da sojojin kasar suka yi da wasu masu dauke da makamai a yankin Arlit na jahar Agadez, a karshen mako.

Dakarun sun kuma kama wata mota, samfarin Land Cruiser, makare da makamai da kuma nakiyoyi, sannan da tsabar kudi kimanin dalar Amirka dubu tasa'in.

Jami'an tsaron na cigaba da farautar wasu karin motocin biyu da suka kai harin.

Tun dai bayan barkewar rikicin Libiya hukumomin Nijar din ke bayyana damuwa game da bazuwar makamai a yankin arewacin kasar.