Kokarin dakile hare-haran Boko Haram

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Hafizu Ringim, ya kaddamar da wasu kayayaki na tabbatar da tsaro a jahar Borno, wadanda suka hada da motoci masu sulke.

Gwamnatin jahar Bornon ce ta samar da wadannan kayayakin, a daidai lokacin da hare-hare da tashin bama-bamai ke yawaita a jaharta ba.

Mutane dayawa ne suka rasa rayukansu sakamakon tashe tashen hankulan, wadanda yawanci ake dorawa kungiyar nan ta Boko Haram.