Gwamnoni a Najeriya na neman karin kaso

Kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kara yawan kason kudaden da gwamnatocin jihohi ke karba daga asusun tarayya.

Kungiyar ta ce, ta yi wannan kira ne domin samun wadatattun kudaden da za su ba gwamnatocin jihohin damar biyan sabon tsarin albashin ma'aikata, tare da gudanar da ayyukan raya kasa.

Jam'iyyar ACN ta goyi bayan a kara yawan kudaden da gwamnatocin jihohin Najeriyar ke karba .

Ta ce, kin yin karin zai janyo matsaloli da dama wadanda za su mummunan tasiri a nan gaba.