Al-Zawahiri ne sabon shugaban Al-Qaeda

Al-Zawahiri Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dama Al-Zawahiri ne mataimakin kungiyar ta al-qaeda

Kungiyar Al-Qaeda ta nada Ayman Al-Zawahiri, wani dadadden na hannun daman Osama Bin Laden, a matsayin sabon shugabanta.

Kungiyar Al-Qaeda dai ta sha alwashin ci gaba abin da ta kira yin jihadi a kan Amurka da Isra'ila da kuma sauran kawayenta, karkashin sabon shugaban nata.

Kwararru sun bayyana Dr al-Zawahiri a matsayin dan kasar Masar, mai matukar hazaka, da kuma ke da tsattsauran ra'ayi.

Tun bayan kashe Osma bin Laden a cikin watan jiya,sakamakon wani samame na dakarun Amurka a Pakistan, aka yi ta hasashen wanda zai karbi ragamar jagorancin kungiyar.