Nijar ta kaddamar da shirin cigaba na shekara biyar

Tutar Nijar
Image caption Shirin ya hada da samar da tasharr nukiliya

A Jamhuriyar Niger, Firaministan kasar, Alhaji Birji Rafini, ya kwashe wunin yau yana bayyana shirin gwamnatinsa na ciyar da kasar ta Nijar gaba a cikin shekaru biyar na tafe.

Muhimmai daga cikin batutuwan da prime ministan ya tabo sun shafi ,Maganar inganta tsaro, yaki da ayyukan ta'addanci da kyautata wa sojojin kasar.

Wani ginshikin siyasar gwamnatin kuwa shi ne , yaki da Fatara da talauci, da bunkasa ayyukan noma domin baiwa yan kasar Niger kwarin gwaiwar ciyar da kansu da kansu.

Ta fannin makamashi kuwa, Firaministan Brigi Rafini ya yiwa yan kasar Niger albishir din soma ayyukan sayarda Man fetur din Niger din a kasuwa a farkon shekara mai zuwa.

A cikin jawabinsa a gaban ga yan majalisar dokokin ,Pirayim Minista Brigi Rafini ya sha alwashin yaki da karbar rashuwa da cin hanci.