Bom ya fashe a hedkwatar 'yan sandan Najeriya

Nigeria Hakkin mallakar hoto nema
Image caption Najeriya ta sha fama da hare-haren bama-bamai a 'yan kwanakin nan

Wani bom da ake zargin dan kunar bakin wake ya tayar a hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya a Abuja, ya haifar da asarar rayuka da dama.

Wani da abin ya faru a gabansa ya shaida wa BBC cewa ya ga gawarwaki sama da 30 tare da motoci fiye da 40 da suka kone.

"An kai harin bom a hedkwatar rundunar 'yan sanda ta kasa, bom ya daidaita wurare da daban - daban," kamar yadda mataimakin mai magana da yawun 'yan sanda Yemi Ajayi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Gidajen talabijin na kasar sun ba da rahoton cewa bom ne ya haifar da fashewar, kuma anga hayaki yana tashi sosai.

Babu tabbas kan adadin mutanen da harin ya ritsa da su.

Boko Haram muke zargi

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Olusola Amore ya ce suna zargin kungiyar Boko Haram da kai harin - wanda ya haifar da ganin gawarwakin mutane a wurin ajiye motoci na hedkwatar 'yan sandan.

"Babu shakka muna zargin kungiyar Boko Haram," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A 'yan kwanakin nan kungiyar Boko Haram ta matsa kaimi wajen kai hare-hare a kan ofisoshin 'yan sanda a Najeriyar.

Ta kuma yi watsi da tayin tattaunawar sulhun da gwamnatin jihar Borno da kuma shugaban Najeriya Goodluck Jonathan suka yi mata.

Najeriya ta sha fama da hare-haren bama-bamai a 'yan kwanakin nan - na farko da aka kai shi ne na ranar da kasar ta yi bikin cika shekaru 50 da samun 'yan cin kai a ranar 1 ga watan Oktoban bara a Abuja.

Karin bayani