Faransa da Jamus na son ceto Girka

Kasar Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sauye-sauyen sun haifar da tashin hankali a Girka

Shugabannin kasashen Jamus da Faransa sun ce suna san a cimma yarjejeniya kan wani sabon shirin ceto tattalin arzukin kasar Girka da aka amince da shi.

Shugaba Sarkozy ya ce ba wani lokaci da za'a bata.

Mr Sarkozy ya ce Faransa da Jamus za su taimakawa kudin Euro da karfin mu: "kuma muna jin tilas ne a samar da wani sabon shirin ceto tattalin arzukin Girka".

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce sun amince su sa matsin lamba wajen ganin an gaggauta yin abin da ya kamata a wajen babban taron kungiyar Tarayyar Turai.

Kasashen na Jamus da Faransa dai su ne suak fi karfin tattalin arziki a jeren kasashen da ke amfani da takardar kudi ta Euro.

Kuma su ne kan gaba wajen daukar duk wani mataki da zai taimaka wajen kare darajar takardar kudin.