Za mu shawo kan hare-haren ta'addanci - Jonathan

Nijeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Najeriya na fuskantar hare-haren bama-bamai a 'yan kwanakin nan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce jami'an tsaron kasar na kokarin shawo kan hare-haren bama-bamai da ya kira na ta'addanci da ake ci gaba da kaiwa a kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara hedkwatar 'yan sanda inda aka kai harin bom jiya, wanda kuma ya yi sandiyar mutuwar mutane da jikkata wasu da dama.

Kungiyar nan ta Ahlus Sunna Lil-da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ta kai harin.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce jami'an tsaron na daukar matakan dakile munanan hare-haren da ke nuna bayyanar abin da ya kira ta'addanci a Najeriya.

Janathan wanda ya bayyanawa manema labarai hakan bayan Sufeto Janar din 'yan sandan Najeriya Hafiz Ringim ya zagaya da shi wuraren da harin ya yi wa barna, ya ce Najeriya za ta shawo kan lamarin hare-haren, don haka kada mutane su razana, domin hare-haren za su zama tarihi nan kusa.

Ba maganar sulhu

"Ba Najeriya ce kadai ta ke fuskantar irn wannan yanayin na hare-hare ba, abu ne da ya zamo ruwan dare in ji shi, don haka babu wata kasa da ta tsira daga irin wannan yanayin".

Editan BBC a Abuja Bashir Sa'ad Abdullahi, ya ce harin na ranar Alhamis shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren bama-bamai da ake kaiwa a kasar a 'yan watannin da suka gabata.

Duka shugaba Jonathan da kuma gwamnan jihar Borno inda kungiyar ta Boko Haram ta fi kai hare-hare, sun nemi kungiyar da ta zo a tattauna domin kawo karshen rikicin.

Sai dai kungiyar ta yi watsi da kiran na su.

Ita dai kungiyar na kira ne da a tabbatar da cikakken tsarin shari'ar musulunci a wasu jihohin Arewacin kasar.

Ayoyin tambaya

Harin dai ya aza ayayoyin tambaya dangane da batun tsaro a kasar. Kuma idan har ta tabbata cewa dan kunar bakin wake ne ya tada bom din, to shi ne harin kunar bakin wake na farko a kasar.

Wakilin BBC Isa Sunusi a Abuja, ya ce a baya dai gwamnatin Najeriya kan kafa kwamitoci domin bincika irin wadannan batutuwa, amma ba tare da an bayyana sakamakon binciken ba.

Daga watan Aprilu na wannan shekara zuwa ranar Alhamis dai an kai hare-haren bama-bamai har sau tara da suka hallaka mutane a sassa daban-daban na Najeriya.

A watan Aprilun da ya gabata kadai an kai hare-haren bama-bamai har sau uku, a jihohin Niger, da Kaduna da Barno da suka kai ga hallaka jama'a.

Koda a watan Mayu da ya gabata, an samu haren-haren bama-bamai da suka hallaka jama'a a jihohin Borno da Zuba a kusa da Abuja, da kuma Zaria a jihar Kaduna da wasu hare-haren a wurare daban-daban a jihohin Bauchi da Barno.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin ya yi sanadiyyar asarar dukiya da kuma rayuka

Shakku kan jami'an tsaro

Cikin wannan watan na Yuni dai hare-haren bama--bamai daban-daban uku aka kai, kuma na ukun shi ne wanda ya fi tada hankalin jama'a, wato harin kunar bakin wake na jiya a harabar babbar hedikwatar 'yan sandan Najeriya.

Ganin cewa koda tushen tsaro a Najeriya bai tsira daga barazanar tsaro ba, 'yan Najeriya na aza ayayoyin tambaya ne akan harkar tsaro baki dayanta a Najeriya.

Wasu masu lura da al'amura dai na nuna damuwa saboda abinda suka kira sakaci, ko rashin sanin makamar aiki daga bangaren hukumomin tsaro da dama da gwamnatin Najeriya take da su, musamman ma ganin yadda harin na jiya ya auku.

Koda kafofin yada labaran Najeriya sun ambato shugaban majalisar dattawan Najeriya, David Mark yana kira ga hukumomin tsaro su binciki kansu, kuma wannan kira nasa ba zai rasa nasaba da yadda masu kai hare-haren bama-baman kan yi nasara wajen aiwatar da duk harin da suka shirya.

Duk da cewa dai kungiyar Boko Haram tace, ita ta kai wannan hari, wani batu dake jan hankali shi ne yadda mutane biyu ke ikirarin cewa, suna magana ne da yawun kungiyar Boko Haram akan wannan batu shi kadai.

Dukka wannan barazanar tsaron na karuwa ne duk da cewa, gwamnatin Najeriya tana kara yawan makuden kudaden da take warewa harkar tsaro, inda koda a ksafin kudin bana aka warewa ofishin mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkar tsaro naira biliyan dari da biyar.

Kamar dai irin wadannan hare-hare da suka auku a baya, wannan karon ma gwamnati tace, tana bincike kan lamarin, amma abinda 'yan Najeriya za su so ji nan bada jimawa ba shi ne sakamakon binciken na baya.

Karin bayani