NATO ta nuna nadama kan kashe farin kaya

Barnar farmaki a Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barnar farmaki a Libya

Rundunar tsaro ta NATO ta bayyana wa BBC cewar ta yi matukar bakin ciki kan duk wata asara da aka tafka ta fararen hula, idan ta tabbata cewar NATOn ce ta kai hari ta sama a wata anguwa ta fararen hula, a Turabulus, babban birnin Libya.

Hukumomin Libyar sun ce mutane bakwai kashe, ciki har da jarirai biyu, a harin da aka kai cikin daren jiya.

Wani mai magana da yawun 'yan tawayen kasar ta Libya a Benghazi shi ma ya bayyana lamarin da cewar, abin takaici ne, duk da cewar NATOn na iya kokarinta wajen kauce ma kai hari a kan fararen hula.