An soke sayar da SONITEL a Nijar

A jamhuriyar Nijar hukumomi sun jingine anniyar su ta sayarda kamfanonin nan guda biyu na sadarwa, SONITEL da Sahel COM, ga wani kamfani na kasar Libya .

Tun a farkon watan Yuni ne dai gwamantin Niger ta jaddada sayarda wadannan kamfanoni ga Kamfanin mai suna GREEN NETWORK mallakar kasar Libya, bayanda kamfanin ya yi nasarar ketare tankade da rairaya domin sayen hannayen wani kaso na hannayen jarin wadannan kamfanoni a bara.

An samu matsala ne bayan da kamfanin ya kasa biyan wasu kudade da ya yi wa gwamnatin Nijar alkawari.

Sayarda wadannan kamfanoni dai ya haddassa tankiya tsakannin wasu kungiyoyin kwadogo da gwamnatin kasar ta Nijar.