An kai hari a Katsina da Borno

A jihar Borno ta Naijeriya an ji musayar wuta da harbe harbe in da jami'an tsaro sukai zargin cewa hare-hare ne daga kungiyar nan da ake kira da Boko Haram.

Tun farko dai a Jihar Katsina wasu mutane da ake zargin 'yan wannan kungiya ne ta Boko Haram sun kai hari a wani cajis ofis na 'yan sanda da kuma wani banki a garin Kankara.

Rahotannin sun ce jami'an 'yan sanda biyar sun hallaka, tare da wani farar hula. An ce maharan sun kwashi makamai, kuma sun saki fursunoni.