Girka ta samu karin tallafi daga Turai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ministan kudi na Girka Evangelios Venizelous

Ministocin kudi na kasashen turai sun cimma matsaya amma basu rattaba hannu ba, akan yarjejeniyar sake baiwa kasar Girka rancen kudade a zagaye na biyu.

Bayan da suka kammala taron da suka yi a Luxembourg a daren jiya, wanda kuma aka gudanar ba tare da wata miskila ba, ministocin sun ce zasu yi kokarin cimma matsaya da kamfanonin dake bin kasar Girkan bashi, da suka hada da Bankuna, asusun fansho da kuma na insora, domin su dage lokacin da kasar zata biya su kudadensu .

Sai dai sun ce domin tabbatar da wannan yarjejeniyar, dole ne kasar Girkan ta rage kudaden da take kashewa da Euro biliyan ashirin da takwas.

Yarjeneniyar tazo ne bayan ministocin kasashen turan sun gudanar da wani taro da mambobin kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki

A gobe talata ne dai ake san Majalisar dokokin Girka zata kada kuria akan sabuwar Majalisar zartarwar da zata sa ido akan kaidoji masu tsauri na baya baya nan.

Sai dai kawo yanzu jama'ar kasar da dama sun ki amincewa da shirin musaman ga wadanda za'a karawa kudin haraji, ko za'a biyasu karamin albashi da kuma wadanda zasu rasa ayukan yi