Gargadi kan makamashin nukiliya

Yukiya Amano Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yukiya Amano na magana ne a wajen taron Hukumar IAEA

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, IAEA, ya yi kira ga kasashen da suka mallaki tashoshin nukiliya da su duba lafiyar tashoshin nan da watanni 18 masu zuwa.

Yukiya Amano yana jawabi ne a wajen wani babban taron hukumar IAEA, a kan batun kiyaye hadurra a tashoshin nukiliya, bayan hadarin da ya faru a tashar Fukushima ta kasar Japan.

Ministoci da kuma masu kula da tashoshin nukiliya daga kasashe dari da hamsin ne ke halartar taron a birnin Vienna na Austria - inda nan ne hedkwatar hukumar ta IAEA.

Mista Amano yace, yanzu jama'a na sun tsorata da sha'anin makamashin nukuliya.

Dan haka ya yi kira ga kasashen duniya su kara kaimi wajen kawar da duk wata illa da makamashin nukiliya ka iya yi ga bil'adama, kuma yace kamata ya yi a yi hakan cikin gaggawa.

Yukiyo Amano ya kuma ce: "Ya kamata duk kasashen da suke da tashoshin makamashin nukiliya su duba yadda za'a tabbatar da cewa ba za su yi wani lahani ba ga bil'adama".

Sai dai kuma shugaban hukumar makamashin nukiluyar ta duniya, ya ce, ana bukatar makuden kudade domin tabbatar da sa ido sosai a kan yadda ake amfani da makamashin nukiliya domin kaucewa duk wata illa ga bil'adama:

Yanzu haka dai babu wani tsari da ya bukaci kasashe su tabbatar da ana amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ba zai yi illa ga bil'adama ba.

Sai dai kuma wasu kasashen na da ra'ayin cewa akwai bukatar a samar da irin wannan tsari.