Makiyaya a Nijar sun yi korafi game da wani sabon shiri na gwamnati

A jamhuriyar Niger wasu kungiyoyin makiyayan kasar ne suka soma korafi game da wani tsari da sabuwar gwamnatin shugabankasa Alhaji Mahamadou Issoufou tace zata bullo dashi domin kirkiro wasu gonakin kiwo na zamani masu suna RANCH a turance.

Manufar wannan shiri dai itace a inganta kiwo ta hanyar kaucewa barin dabbobin yin gararamba a dazuzzuka.

Hakan dai a cewar hukumomin kasar zai baiwa makiyayan damar bada cikakkiyar kulawa ga dabbobinsu, tare da hana dabbobin fadawa cikin matsalolin da suka shafi karancin ruwa da ciyawa, lamarin da kan janyowa makiyayan asara mai dimbin yawa.

Sai dai Makiyayan sun bayyana tsarin da sabuwar gwamnatin kasar ke shirin kirkirowa da cewa ba zai yi wani tasiri a kansu ba, suna masu cewar galibinsu nada karamin karfi, a saboda haka suka ce masu hali ne kadai zasu ci gajiyar wannan shirin.