Tarayyar Turai ta dage takunkumin da ta sanyawa Nijar

Tutar tarayyar turai Hakkin mallakar hoto No credit

Hukumar tarayyar turai ta dage takunkumin hana bayar da taimakon da ta sanyawa Jamhuriyar Niger.

Sanarwar ta ce hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda yadda sojoji suka mayar da mulki zuwa ga hannun farar hulla a kasar.

A cikin shekarar 2009 ne hukumar tarayyar turan ta sanya takunkumin hana bada taimakon, bayan da tsohon Shugaban kasar, Mamadou Tanja ya sauya tsarin mulkin kasar domin zarcewa akan karagar mulki.