'Yan gwagwarmaya za su cigaba da zanga-zanga a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan gwagwarmaya a Syria sun ce zasu cigaba da zanga zangar nuna kyamar gwamnati, bayan da suka yi watsi da wani jawabin da shugaba Bashar al Assad yayi, inda yake cewa zai bude tattaunawa tsakanin 'yan kasar.

'Yan mintoci bayan jawabin nasa, sabuwar zanga-zanga ta barke a biranen kasar da dama.

Wani kakakin masu fafutukar ya ce, a yanzu ba wai kawai suna son a yi sauye-sauye a kasar bane, a'a, suna kuma bukatar sauyin gwamnati.