Safarar miyagun kwayoyi a yammaci Afrika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu daga cikin miyagun kwayoyin da aka kwace

Majalisar dinkin duniya ta ce ana ci gaba da samun hodar ibilis a iyakokin yammacin Afrika yayin da hukukomin tsaro ke kokarin kawo karshen harkar cinikayyar da aka yi kiyasin ta kai kusa da dala biliyan daya.

Wasu mutane kalilan da basu wuce su dari ba daga yankin Latin Amurka na amfani da yammacin Afrika a matsayin wata tashar safarar miyagun kwayoyi amma an yi ammana cewa akwai mutanen yammacin Afrika da dama dake da hannu a cikin wannan harka.

Bugu da kari miyagun kungiyoyi masu safarar kwayoyi sun fara kunno kai a yankin, kuma suna kokarin ganin sun sha gaban hukumomi masu yaki da muggan laifuka da ke wahala wurin kama kwayoyin da ake safara da su.

Alkaluman baya-bayanan nan na nuni da cewa adadin kwayar hodar ibilis da aka kwace ya ragu daga tan 47 zuwa tan 37 tsakanin shekerar 2008 zuwa 2009.

Sai dai Majalisar dinkin duniya ta ce lamarin ba haka yake ba dangane da cinikiyya ta haramtacciyar hanya da ake yi da kwayar .