Gwamnatin Girka ta samu kuriar nuna goyon baya

Girka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Girka ta samu kanta a halin tsaka mai wuya

Gwamnati Girka ta tsallake shinge na farko, yayinda da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada kuri'ar nuna goyon baya kan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

A lokacin da suka tafka mahawarar a cikin zauren majalisar firaministan kasar George Papandreuo ya ce idan kasar bata shawo kan matsalar basusukan da take fuskanta ba, kuma ta fice daga tsarin amfani da kudi na bai daya to hakan kan iya janyoma kasar wani bala'i

Firaministan ya nemi hadin kan jama'ar kasar duk da rarabuwar kawunan dake tsakaninsu

Sai dai a wajen majalisar dubun dubatar masu zanga zanga sun rika kade kade da rera wakokin nuna rashin amincewa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Za'a dai iya cewa bukatun masu bada rance a tarayar turai da kuma sauran kasashen duniya yasa tsarin siyasar kasar cikin tsaka me wuya.Ko dayake shugaban hukumar turai ya ce wanan wani lokaci ne da za'a bayana gaskiya ,amma zai kasance kuskure idan aka rena anniyar shugabannin siyasar turai na ganin sun kare kudin Euro .