Masu zanga zanga sun ja daga, yayin da gwamnatin Girka ke fuskantar kuri'ar goyon baya

Wani mai zana zanga a Kasar Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai zana zanga a Kasar Girka

Masu zanga zanga a kasar Girka na kara taruwa a gaban majalisar dokokin kasar, yayin da gwamnati ke jiran majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar goyon baya a cikin 'yan sa'o'i kadan.

Masu zanga zangar na ta rera wakokin kin amincewa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da kuma yanayin siyasar kasar baki daya:

Wani wakilin BBC a Athens ya ce ba wasu mutane ne masu yawan gaske ba, amma kuma suna wakiltar takaicin jama'a kan matsalar tattalin arzikin da tai wa kasar dabaibayi.

Kasar ta Girka dai na fadi tashin kauce wa kasa biyan bashin da yayi mata katutu a cikin wata mai zuwa.

Girka dai na bukatar a samar da wani sabon shirin ceto tattalin arzukin ta a karo na biyu, sai dai kuma hakan zai dogara kan kara rage kudaden da kasar ke kashewa.